logo

HAUSA

Kara cudanya maimakon katse hulda mafita ce ga tattalin arzikin duniya

2022-05-19 21:43:02 CMG Hausa

A yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi ta kafar bidiyo, a taron cika shekaru 70 da kafuwar hukumar yayata hada-hadar cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin a jiya Laraba, wanda kuma shi ne taron kolin kasa da kasa na ingiza harkokin cinikayya da zuba jari, shugaban kasar Sin ya jaddada cewa, ya dace a rungumi yin shawarwari maimakon yin fito-na-fito, da kara hada kai maimakon kawo cikas, da kara cudanya maimakon katse hulda, da kara nuna hakuri maimakon nuna wariya, ta yadda za’a iya jagorantar aikin yin gyare-gyare ga tsarin gudanar  da harkokin duniya bisa ra’ayin shimfida adalci.

Sakamakon rikicin siyasar kasa da kasa, da kara yaduwar cutar COVID-19, tattalin arzikin kasa da kasa na fuskantar koma-baya. Ko ina mafita ga tattalin arzikin duniya? Amsar hakan na cikin kiran da shugaba Xi ya yi, wato “kara cudanya maimakon katse hulda”.

Ra’ayin dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya na samun karbuwa sosai a duniya, amma yana fuskantar tsaiko a yanzu, ganin yadda wasu mutane daga yammacin duniya ke yunkurin rura wutar rikici, cewa ya kamata a “katse hulda” da kasar Sin.

Amma hakikanin gaskiya ta shaida cewa, maganar “katse hulda” ba daidai ba ne. A shekara ta 2021, jimillar kasuwancin da kasar Sin ta yi da kasar Amurka ta karu da kusan kaso 30 bisa dari, wadda ta kai dala biliyan 755.6. Haka kuma bangarori daban-daban a Amurka, sun yi kira da a soke karin harajin kwastam da aka bugawa hajojin kasar Sin, don magance matsalar hauhawar farashin kaya.

Dukkanin wadannan sun tabbatar da cewa, zama tsintsiya madaurinki daya, abu ne da ba za’a iya kaucewa ba a halin yanzu, kuma sake farfado da kasuwanci, da zuba jari, su ne babban karfin murmurewar tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)