logo

HAUSA

An fara taron koli na biranen Afirka a gabar da ake kira a hanzarta sabunta birane

2022-05-18 10:48:27 CMG Hausa

Jiya ne, aka bude taron koli na biranen nahiyar Afirka a birnin Kisumu dake yammacin kasar Kenya, a daidai lokacin da ake kira da a kara zage damtse, don inganta sabunta birane, domin tinkarar fatara da cututtuka da kuma karfafa juriyar al'ummomin yankunan nahiyar.

A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya jaddada cewa, tsare-tsare masu inganci, da samar da kudade na zamani, da yin hadin gwiwa, su ne manyan hanyoyin samun ci gaba mai dorewa a birane a nahiyar Afirka.

Taron na kwanaki biyar, ya hallara wakilai sama da 4,000, da suka hada da tsoffin shugabannin kasashe, da na gwamnatoci, da ministocin kananan hukumomi, da masu unguwanni,da masu bincike da kuma ’yan kasuwa.

Taron wanda aka gudanar bisa taken "Rawar da masu shiga tsakani na kasashen Afirka ke takawa wajen aiwatar da ajandar MDD nan da shekarar 2030 da ajandar kungiyar Tarayyar Afirka game da raya nahiyar nan da shekarar 2063", ana sa ran zai fito da wata sabuwar taswirar gaggauta sabunta birane a nahiyar. (Ibrahim Yaya)