logo

HAUSA

Lai Mohammed ya ja kunnen kamfanoni mamallaka dandalolin sada zumunta da su daina ba da damar rura wutar rikici

2022-05-18 20:44:03 CMG Hausa

Ministan watsa labarai da raya al’adu na Najeriya Lai Mohammed, ya ja kunnen kamfanoni mamallaka dandalolin sada zumunta, da su daina baiwa kungiyar nan ta IPOB, ta ‘yan aware dake kudu maso kudancin Najeriya, damar yada bayanai na rura wutar rikici, da kabilanci a kan shafukan su.

Lai Mohammed ya yi wannan gargadi ne a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya a jiya Talata, yayin wata tattaunawa da tawagar kamfanin Facebook.

Mohammed ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya za ta sanya ido sosai kan shafukan Facebook, da sauran dandaloli makamantan sa a kwanaki masu zuwa, domin tabbatar da ko facebook din ya kiyaye wannan jan hankali, yayin da kasar ke kara azamar yayata manufar amfani da dandalolin sada zumunta ta hanyoyin da suka kamata.

A cewar sa, an riga an ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda, don haka babu wani dalili da zai sa Facebook ya rika baiwa kungiyar damar shiryawa, ko gabatar da farfagandar kiyayya, ko wargaza zaman lafiyar Najeriya. (Saminu)