logo

HAUSA

Gwamnatin Ghana ta bukaci al’umma su kara sa ido da nufin dakile ayyukan ta’addanci

2022-05-18 11:04:12 CMG Hausa

Gwamnatin Ghana ta bukaci al’ummarta su kara sa ido yayin da ake kara samun barazanar ta’addanci a kasar ta yammacin Afrika.

Wata sanarwa da ministan tsaron kasar Albert Kan-Dapaah ya fitar a jiya, ta bukaci al’umma su kara taka tsantsa game da tsaronsu a wuraren taron jama’a.

A cewar ma’aikatar tsaron kasar, kiran na zuwa ne yayin da ake da dalili mai kwari dake nuna cewa ’yan ta’addan dake yankin, na neman farwa kasar ta Ghana, don haka akwai bukatar inganta matakan tsaro da kira ga al’umma da su kara kula.

Gwamnatin ta kuma tabbatarwa al’ummar cewa, hukumomin tsaro da dukkan wadanda ke da hakkin tabbatar da tsaro a kasar, na aiki tukuru domin tabbatar da tsaron kasar da al’ummarta. (Fa’iza Mustapha)