logo

HAUSA

BBC ta kitsa karairayi kan batun ta’addanci

2022-05-18 21:57:31 CMG Hausa

Kwanaki sama da 20 da suka gabata, an kai farmakin ta’addanci kan wata mota ta kwalejin koyon harshen Sinanci, wato Confucius Institute dake jami’ar Karachi dake kasar Pakistan, al’amarin da ya haddasa mutuwar wasu malaman kasar Sin uku, tare da jikkata wani.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da irin wannan farmakin da kakkausar murya. Amma ita kafar yada labaran BBC, ta wallafa wasu rahotanni kwanan nan, inda ta yi yunkurin wanke wadanda suka kai farmakin daga mummunan laifin da suka aikata.

A matsayinta na daya daga cikin kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya da suka taka rawa, abun da BBC ta yi, ba imani cikin sa ko kadan, wanda ya sa ta zama abokiyar gaba ga duk wani dake son shimfida zaman lafiya a duniya.

Ko me ya sa wasu kafofin watsa labarai, kamar BBC, su kan nuna fuska biyu? Hakikanin gaskiya ita ce, wadannan kafofin yada labaran suna dogara kan manyan masu hannu da shuni na kasashen yamma, kana, a kasashen yamma, dukiyoyi da siyasa hade suke. A sabili da haka, ta hanyar fakewa da “neman ‘yancin yada labarai”, wasu kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya suna nasu aiki, domin bautawa masu kudi da masu iko.

Yanzu ana iya fahimtar dalilin da ya sa wasu kafafen yada labaran yamma, suka yi yunkurin ruwaito rahotanni, game da wasu jita-jitar da aka yada dangane da batutuwan da suka shafi Xinjiang da Hong Kong, sa’annan sun yi shiru, a yayin da wasu ke son bayyana gaskiyar abubuwan dake faruwa a Xinjiang da Hong Kong. (Murtala Zhang)