logo

HAUSA

Hadin kan Sin da Afirka a fannin samar da Ilimi Sana’o’i ga matasa

2022-05-18 08:39:02 CMG Hausa

A kwanan baya ne, kungiyar mu’ammala ta fuskar ba da ilimi ta kasar Sin, ta kira wani taro na ingiza shirin ba da ilimin sana’o’i tsakanin Sin da Afrika, kuma taron kafa kungiya a wannan fanni ta kafar bidiyo da kuma zahiri, don tabbatar da shawarwarin hadin kan Sin da Afrika, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika.

Mataimakin daraktan sashin hadin kan kasa da kasa, da yin mu’amala na hukumar ba da ilmi na Sin Jia Peng, ya taya murnar kafuwar kungiyar. Ya kuma ce makomar nahiyar Afrika ita ce matasa, kuma mafitar matasa ita ce samun ilimi, wanda daga karshe zai taimaka ga ci gaban al’umma baki daya.

Sanin kowa ne cewa, gwamnatin Sin ta dade tana dora matukar muhimmanci kan hadin kan bangarorin biyu ta wannan fuska, musamman ma a fannin ba da ilimi na sana’a, abin dake da makoma mai haske wajen hadin kansu. Sin na fatan kafa tsari mai yakini da kasashen Afrika cikin dogon lokaci, don goyon bayan shiri mai taken “Makomar Afrika: hadin kan Sin da Afrika kan samar da ilmi na sana’a”, ta yadda za a horas da kwararru a fannin samar da kayayyaki da raya tattalin arziki na yanar gizo, da  sauran sabbin sana’o’i.

Kasancewar matasa a matsayinsu na kashin bayan ci gaban kowace al’umma, samar musu da abin dogaro da kai, zai taimaka matuka wajen rage zaman kashe wando, wanda a mafi yawan lokuta kan kai da shigar irin wadannan matasa ga kungiyoyin ’yan ta’adda ko wasu ayyuka marasa kyau dake iya lalata musu rayuwa da ma haifar da mummuna sakamako a cikin al’umma.

Masu fashin baki na cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka a wannan fanni, ya kara tabbatar da sahihancin alakar sassan biyu, da ma cika alkawarin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta horas da matasan nahiyar, ta yadda za su kasance masu dogaro da kansu a fannin sana’a.  (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)