logo

HAUSA

Bankin Duniya zai sake samar da kudaden ayyukan kyautata rayuwar matalauta a Sudan

2022-05-18 11:16:11 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana cewa Bankin Duniya ya sanar da hukumomin kasar cewar, zai sake maido da shirin samar da kudaden gudanar da ayyuka don tallafawa mutanen dake fama da talauci a kasar Sudan.

Ma’aikatar ta sanar cewa, bankin duniya yana cigaba da bin matakan sake maido da shirin gudanar da ayyukan, wadanda za su mayar da hankali kai tsaye wajen tallafawa matalautan kasar Sudan, kamar shirin nan na 'Thamrat', da na riga-kafin annobar COVID-19 ta hanyar aiwatarwa da kuma sanya ido, inda wasu bangarori za su dinga bibbiyar ayyukan kamar sashen shirin samar da abinci na MDD.

Shirin "Thamrat" ya kasance daya daga cikin shiri mafi muhimmanci da bankin duniya ke samar da kudaden gudanarwa, da nufin rage radadin mummunan tasirin shirin farfado da tattalin arzikin kasar wanda rusasshiyar gwamnatin rikon kwaryar kasar Sudan ta amince da shi.

Gwamnatin tsohon firaministan kasar Sudan Abdalla Hamdok, ne ta kaddamar da shirin tallafin a shekarar 2020, inda aka tsara samar da kudade na kai tsaye ga mutanen Sudan kusan miliyan 32, daga cikin jimillar adadin ’yan kasar miliyan 40. (Ahmad)