logo

HAUSA

Masu fafutuka na Afirka sun bayyana cewa biranen da ke kiyaye sauyin yanayi na da muhimmanci wajen gaggauta bunkasuwa

2022-05-17 10:21:02 CMG Hausa

 

Masu fafutuka sun bayyana cewa, takaita fitar da iskar Carbon mai gurbata muhallin duniyarmu a biranen Afirka dake saurin samun bunkasuwa, zai taimaka wajen kawar da matsalar sauyin yanayi, kamar ambaliyar ruwa, baya ga gaggauta tabbatar da samar da makoma mai adalci ta bai daya maras gurbata muhalli ga nahiyar.

Masu fafutukar sun bayyana haka ne jiya Litinin, gabanin taron kolin biranen Afirka karo na 9 da aka shirya gudanarwa daga yau Talata 17 zuwa 21 ga watan Mayu a birnin Kisumu dake yammacin kasar Kenya.

Darektan riko na kungiyar dake yaki da sauyin yanayi ta Afirka (PACJA) mai hedkwata a Nairobin Kenya, Charles Mwangi ya jaddada cewa, yayin da nahiyar ke ci gaba da bunkasa cikin sauri, akwai bukatar gaggauta tabbatar da kiyaye sauyin yanayi da muhimman ababen more rayuwa, domin kare lafiya da makomar mazaunanta.

Ya ce, na kwanaki biyar, zai baiwa nahiyar damammakin gano sabbin kirkire-kirkire, da za su taimaka wajen kiyaye matsugunan biranen nahiyar daga gurbata, a matsayin hanyar cimma muradun MDD nan da shekarar 2030.

A bisa taken taron "Rawar da masu shiga tsakani na biranen kasashen Afirka ke takawa, wajen aiwatar da ajandar shekarar 2030 ta MDD da ajandar raya nahiyar Afirka nan da shekarar 2063 ta kungiyar Tarayyar Afirka 2063," taron zai kuma tattauna sabbin dabarun inganta sabunta birane a nahiyar. (Ibrahim Yaya)