Abdoulkarim Muhamat: Ina fatan za’a kara hadin-gwiwa tsakanin Nijar da Sin
2022-05-17 14:59:54 CMG Hausa
Abdoulkarim Muhamat, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar ne, wanda a yanzu hake yake aiki a fannin daukar ma’aikata wato HR, a kamfanin GWDC na kasar Sin dake Nijar, wato Great Wall Drilling Company.
A zantawarsa da Murtala Zhang, Abdoulkarim Muhamat, ya yi tsokaci kan fahimtarsa game da yare da al’adun kasar Sin, da yadda yake mu’amala da mutanen kasar ta hanyar aiki tare da su.
A karshe, Abdoulkarim Muhamat ya yaba da irin hadin-gwiwa da ake yi tsakanin Jamhuriyar Nijar da kasar Sin, musamman a fannin hako ma’adinai. (Murtala Zhang)