logo

HAUSA

MDD da AU sun yaba da gudanar zabukan Somaliya cikin kwanciyar hankali

2022-05-17 10:36:51 CMG Hausa

 

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yaba da yadda zaben shugaban kasar Somaliya ya gudana lami lafiya a ranar Lahadi. Yana mai taya Hassan Sheikh Mahamud murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar na 10.

Cikin wata sanarwa, sakatare janar din ya bayyana fatan sabon shugaban zai gaggauta kafa gwamnatin da za ta kunshi dukkan bangarori. Yana kuma fatan sabuwar gwamnatin da mambobin majalisar kasar, za su hada hannu wajen mayar da hankali kan muhimman batutuwan kasa da shawo kan kalubalen da take fuskanta.

Cikin wata sanarwa ta daban, shugaban hukumar Tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat ya taya Hassan Sheikh Mohamud murnar lashe zaben shugaban kasar Somaliya.

Moussa Faki Mahamat ya kuma yabawa al’ummar Somaliya, bisa yadda suka nuna matukar kishin kasa wajen gudanar da zaben cikin lumana, tare da yabawa jami’an tsaron kasar da na shirin wanzar da zaman lafiya na AU wajen tabbatar da tsaro yayin zaben.

Ya kuma jaddada cewa AU za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da Somaliyar ke yi na zurfafa demokradiyya da wanzar da sulhu da zaman lafiya da kuma tsaro a kasar. (Fa’iza Mustapha)