logo

HAUSA

Gwamnatin wucin gadi ta kasar Mali ta dakile wani yunkurin juyin mulki

2022-05-17 14:19:41 CMG Hausa

Gwamnatin riko ta kasar Mali ta sanar a jiya cewa, hukumar tsaron kasar ta cimma nasarar dakile wani yunkurin juyin mulki.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa, wasu sojojin kasar sun yi yunkurin juyin mulki ta matakan soja, daga daren ranar 11 zuwa daren ranar 12 ga watan nan, kuma, wadannan sojoji sun sami goyon baya ne daga wata kasa ta yammacin duniya. Haka kuma, gwamnatin ta yi Allah wadai da wannan mataki da kakkausar harshe, bisa yadda matakin ke bata yanayin zaman lafiya da tsaron kasar. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, burin juyin mulki shi ne, hana ci gaban yunkurin sake gina kasa da dawowar tsarin mulkin kasa baki daya.

Bugu da kari, a halin yanzu, gwamnatin rikon ta kasar Mali tana gudanar da bincike don neman wadanda suke goyon baya wannan mataki. Amma, ba a yi karin bayani kan ko an kama wasu mutane ba ko a’a. Kazalika ba a yi karin bayani kan sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki ba. (Maryam)