logo

HAUSA

Sanarwar ministocin kungiyar G7 ta keta ka’idar kasa da kasa ce dake neman rura wutar rikici

2022-05-17 17:21:40 CMG Hausa

A baya-bayan nan ne, ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 suka fitar da wata sanarwa bayan taron da suka yi, inda a cikinta suka bayyana wasu bukatu ga kasar Sin, wadanda suka yi su bisa son zuciya da zarge-zarge marasa tushe, da gazawa wajen mutunta cikakken ’yancin kan kasar.

Cikin sanarwar, sun ce sun damu da yanayin kwanciyar hankali a tsibirin Taiwan. Amma sam kasashen yamma ba su damu da hakan kamar yadda suke furtawa ba. Sanin kansu ne cewa, zaman lafiyar yankin ya dogara ne da janyewarsu daga yi wa harkokin gidan Sin katsalandan da kuma mutunta manufar kasar Sin daya tak a duniya da kauracewa bi ta bayan fage wajen kulla wata alaka da yankin, wanda mallaki ne na kasar Sin, da kuma daina ingiza wasu tsiraru wajen rajin neman ballewa. 

Har ila yau, sun tabo batun Xinjiang da Tibet, suna masu cewa a kare hakkokin bil adama a yankunan. Hakika kasashen yammacin duniya su kan manta cewa, gwamnatin da tsarin demokradiyyar kasar Sin, su kan sanya al’umma ne a gaban komai. Kasar Sin ba ta maraba da duk wani abu da zai taba walwalar al’ummarta. Kana mai daki shi ya fi kowa sanin idan yake yoyo, wato mutanen wadannan yankunan ne ke da alhakin korafi ba wasu daga waje ba. Kasar ta sha nanata cewa tana maraba da kasashen nan su ziyarci yankunan don ganewa idonsu yanayin da suke ciki, amma maimakon hakan, sai suke zama suna kitsa karairayi da zummar shafa mata bakin fenti.

Bugu da kari, sun tabo batun Hong Hong da kare hakkin bil adama da demokradiyya a yankin. Idan ba a manta ba, irin wadannan furuci ne suka haifar da tashe-tashen hankula a yankin na Hong Kong a shekarun baya, wannan alama ce karara dake nuna cewa, ba kaunar mutanen Hong Kong din da zaman lafiyarsa suke ba. Idan da sun damu, da ba za su taba ingiza bata gari wajen tayar da hankalin jama’a ba, lamarin da ya haifar da asarar dukiyoyi da tattalin arzikin yankin.  

Ba sai an fada ba, irin wadannan kalamai da kasashen yammacin duniya suke kan kasashen da suke ganinsu a matsayin barazana da suka zabi neman hanyar raya kasa da ta dace da yanayinsu, bai taba haifar da wani da mai ido ba, illa kara rura wutar rikici da kawo tsaiko ga kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya  da haifar da yake-yake. (Faeza Mustapha)