logo

HAUSA

Wa zai yarda Amurka ta goyi-bayan yankin Taiwan don halartar babban taron lafiya na duniya?

2022-05-17 20:57:04 CMG Hausa

A gabannin babban taron kasa da kasa kan harkokin kiwon lafiya karo na 75, wasu ‘yan siyasar Amurka sun sake kulla makirci, na nunawa yankin Taiwan goyon baya don halartar taron.

Kwanan nan ne, shugaban Amurka ya sa hannu kan wani shirin doka, inda ya bukaci sakataren harkokin wajen kasar, da ya taimaki yankin Taiwan, don sake dawo da matsayinsa na dan kallo a hukumar WHO, ta yadda zai samu damar halartar taron. Irin wannan abu, shisshigi ne da aka yi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda kuma ya sabawa babbar manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da ka’idojin wasu sanarwar hadin-gwiwa uku da aka daddale tsakanin Sin da Amurka.

Baya ga wasu ‘yan kasashe kalilan da suka kulla huldar diflomasiyya tare da Taiwan, gami wasu kasashen yammacin duniya kadan, babu wata kasa da ta goyi bayan Amurka.

Batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne mafi muhimmanci a dangantakar Sin da Amurka, wanda ya shafi babban muradun kasar Sin. Ya dace kasar Amurka ta cika alkawarin siyasar da ta daukawa kasar Sin, ta dakatar da kawo illa ga babbar manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, don tabbatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma tare. Yin fuska biyu kan batun Taiwan da Amurka ta yi, zai kara kawo illa ga kwarjininta a fannin siyasa. (Murtala Zhang)