logo

HAUSA

Kiwon dabbobi a gida yana taimakawa kiwon lafiyar kwakwalwar tsofaff

2022-05-17 09:27:16 CMG Hausa

 

Sakamakon nazari da hukumar ilmin cututtukan da suka shafi jijiya ta kasar Amurka ta kaddamar a kwanan baya ya nuna cewa, kiwon dabbobi kamar kare, kyanwa a gida yana taimakawa rage saurin lalacewar kwarewar fahimta ta tsofaffi, don haka yana da amfani wajen kiwon lafiyar kwakwalwar tsofaffi.

Masu nazari daga jami’ar Michigan ta kasar Amurka sun tantance bayanan da suka shafi lafiyar tsofaffi dubu 1 da dari 3 da 69 wadanda matsakaicin shekarunsu suka kai 65 da haihuwa. A farkon lokacin da aka kaddamar da nazarin, wadannan tsofaffi ba su da wata matsala wajen fahimtar abubuwa, kana kuma wasu kaso 53 cikin dari ne daga cikinsu suke kiwon dabbobi a gida, wasu kaso 32 cikin dari ne daga cikinsu suka dauki shekaru fiye da 5 suna kiwon dabbobi a gida. Wadannan tsofaffi sun shiga jarrabawar kwarewar fahimta a fannoni da dama, alal misali, kidayar abubuwa da riko da kalmomi da dai sauransu. masu nazarin sun yi amfani da sakamakon jarrabawar don bada maki daga sifiri zuwa 27 dangane da kwarewar fahimta.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, bayan shekaru 6, in an kwatanta su da wadanda ba su kiwon dabbobi a gida, lalacewar kwarewar fahimta ta tsofaffin da suke kiwon dabbobi a gida ba ta da sauri sosai. Musamman ma wadanda suka dade suna kiwon dabbobi a gida. Bayan shekaru 6, matsakaicin makin da tsofaffin da suka dade suna kiwon dabbobi a gida suka samu ta fuskar fahimtar abubuwa ya fi wadanda ba su kiwon dabbobi a gida yawa har 1.2.

Dangane da nazarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani da cewa, da ma, an gano cewa, kiwon dabbobi a gida yana da amfani a fannin kiwon lafiya, kamar rage hawan jini. Sabon nazarin ya nuna mana cewa, kiwon dabbobi a gida yana taimakawa kaucewa lalacewar kwarewar fahimta. Watakila matsin lambar da ake fuskanta ya haifar da illa ga kwarewar fahimta, amma kiwon dabbobi a gida yana amfanawa wajen sassauta matsin lambar da ake fuskanta. Ban da haka kuma, mai yiwuwa kiwon dabbobi a gida ya sanya masu kiwon kara motsa jiki, ta yadda zai amfanawa lafiyar kwakwalwa. (Tasallah Yuan)