logo

HAUSA

Li Sufang: Kokarin raya aikin surfani mai salon kabilar Yao bisa sabbin fasahohi

2022-05-17 10:43:46 CMG Hausa

Li Sufang, shugaba kuma mai tsara fasalin tufafi na kamfanin Guoshan Yaojia na Guangxi dake gundumar Babu ta birnin Hezhou a jihar kabilar Zhuang ta Guangxi mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta samu dimbin nasarori wajen yayatawa da raya surfani mai salon kabilar Yao cikin shekaru 10 da suka gabata. A lokacin zafi na shekarar 2021, cibiyar kayayyakin ado na gargajiya na kabilar Yao, wadda Li Sufang ta kafa, ya sayi wani injin surfani da saurinsa ya ninka masu aikin surfani da hannu har sau 100.

An haifi Li Sufang ne a shekarar 1979, inda iyayenta suka kasance masu aikin hannu. Ta fara koyon yadda ake surfani ne daga mahaifiyarta, tun tana karama.

A shekarar 2006, kasar Sin ta sanya fasahar tsara tufafi da kayayyakin ado na kabilar Yao cikin jerin kayayyakin gargajiya da aka yi gado na kasar. Wannan ya zaburar da Li  Sufang wajen kafa kamfani, ta yadda za ta iya bada tata gudunmuwa wajen farfado da tufafi da kayayyakin ado na kabilar Yao a garinsu.

A shekarar 2007, Li Sufang ta koma garinsu bayan ta shafe shekaru 7 tana aiki a Hangzhou, babban birnin Lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin. Ita da mijinta Liu Degan, sun kafa wajen dinkin tufafi guda biyu a gundumar Babu, inda suke tsara tufafi da kayayyakin ado na Kabilar Yao.

Li Sufang ta ce, “Ya kamata mu yi kokari mu kare tufafi da kayayyakin ado na gargajiya na kabilar Yao, wadanda su ne tushen al’adunmu. Yayin da al’ummar Sinawa ke samun ci gaba cikin shekarun da suka gabata, an samu sauye-sauye cikin yanayinsu na rayuwa da zamantakewa da tsarin ado. Domin biyan bukatun tsarin ado na mutanen zamani, mun kara siffofin zamani da kwalliya cikin kayayyakinmu. Wannan, ya bunkasa raya fasaharmu ta gargajiya.”  

Li Sufang ta kara da cewa, an yi gadon siffofin surfani dake kan kayayyakin gargajiya na kabilar Yao masu ban sha’awa daga zuri’a zuwa zuri’a, kuma kowannensu na dauke da ma’ana, wadda ita ce tushen al’adun kabilar Yao. “Domin cimma bukatun matasa, na sauya yaduka ko launikan kayayyakin. Na kuma jagoranci ma’aikatana wajen samar da wasu kayayyakin bukatun yau da kullum, kamar jakukunan mata da sauran wasu kayayyakin ado,” a cewarta.

A shekarar 2016, Li Sufang ta kafa wata cibiya ta gadon tufafi da kayayyakin ado na gargajiya na kabilar Yao. Bisa yadda kamfaninta ke samun tagomashi, Li Sufang ta samu damar daukar mata da dama aiki. Wannan ya taimakawa dimbin iyalai shawo kan kalubalen rashin kudi da suke fuskanta. Kamfanin na tattara surfani da kayayyakin gargajiya na kabilar Yao da matan suka samar, sai kuma ya gyara su kafin ya sayar. Saboda amfani da injin surfani na zamani da ci gaban da aka samu wajen fasalta kayayyaki, kamfanin ya samu ingantuwa ta fuskar gudanar da ayyuka, da kuma raguwar kudin da yake kashewa wajen samar da kayayyaki. 

Bisa yadda Li Sufang da ma’aikatanta ke jajircewa wajen yayata kayayyakin ado da tufafin gargajiya na kabilar Yao, kayayyakin sun samu karbuwa a fadin kasar Sin. A kowanne lokacin biki ko hutu, za a ga matasa ‘yan kabilar Yao sanye da kayayyakin gargajiya masu ban sha’awa.

Li Sufang ta ce, “tun bayan bude shago a gundumar Babu, dukkan amare da angwaye na kauyenmu, suna son sanya tufafin gargajiya a lokacin bikinsu. kafin sannan, da wuya ake ganin mutanen kauyen da tufafin gargajiya masu ban sha’awa, domin ba sa iya samun wurin da ake iya samun wadannan kayayyaki na alfarma, haka ma da wuya ake samun masu yinsu. Yanzu, kusan kowanne iyali na kauyenmu na da tufafin da kayayyakin adon.” 

Domin raya al’adar ta fasahar gargajiya, cikin shekaru da dama da suka gabata, Li Sufang ta jagoranci ma’aikatanta wajen fasalta kayyakin kabilar Yao masu kyan gani, da aka yi musu ado da siffofin surfani daban-daban. Saboda kyan surfanin da kwarewar aikin, mutane da dama daga fadin duniya, sun yi sha’awar kayayyakin da kamfanin ya samar. An kuma sayar da su a kasashe da dama, ciki har da Faransa da Amurka. Saboda yabawa gagarumar gudunmuwarta ga yayata al’adar a duniya, an yi wa Li Sufang lakabi da babbar mai fasaha a jihar Guangxi, kuma wadda ta yi gadon tufafi da kayayyakin gargajiya na kabilar Yao a matakin birnin Hezhou.

Cikin ‘yan shekarun da suka gabata, Li Sufang ta jagoranci ma’aikatanta wajen kirkiro kayayyakin kula da lafiya. Misali, sun samar da kayyakin samar da dumama jiki daban-daban, ciki har da matashi da makarin gwiwa da kugu da wuya, wadanda aka kunshe magungunan gargajiya na kabilar Yao a cikinsu, suka kuma yi musu ado da surfani masu siffofi daban-daban.

Bisa la’akari da ci gaban da kamfanin Li Sufang ya samu, ya samar da guraben ayyukan yi sama da 600 ga matalauta da ‘yan ci rani, wadanda suka dawo gida domin neman aiki. Mazauna da dama da ma’aikata sun samu riba daga aikin surfani. Li Sufang ta yi alkawarin kara zage damtse wajen jagorantar ma’aikatanta kara kirkiro kayayyakin da za su bayyana alamomin al’adun al’ummar kabilar Yao. (Kande Gao)