logo

HAUSA

Majalisar dokokin Somaliya ta sake zabar tsohon shugaban kasar

2022-05-16 10:25:12 CMG Hausa

Tsohon shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, ya sake zama sabon shugaban kasar na 10, bayan da majalisar dokokin kasar ta sake zabarsa a matsayin shugaban Somaliya, inda ya kada shugaban kasar mai ci Mohamed Farmajo, a zagaye na uku na zaben da aka gudanar a ranar Lahadi Mogadishu, babban birnin kasar.

Farmajo yana neman a sake zabarsa ne domin ya shugabanci kasar a wa’adin mulki karo na uku, inda ya amince da shan kaye a zaben a hannu Mohamud.

Mohamud dan shekaru 67 a duniya, wanda ya taba rike shugabancin kasar tsakanin shekarun 2012-2017, ya zamto shugaban kasa na farko da aka zaba sau biyu a tarihin kasar Somaliya. (Ahmad)