logo

HAUSA

MDD ta yi gargadin kara tabarbarewar fari a nahiyar Afirka cikin shekaru 40

2022-05-16 10:20:20 CMG Hausa

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da tsare-tsaren ayyukan ba da agaji jin kai na Martins Griffiths, ya yi gargadi kan kara tabarbarewar matsalar fari a yankin kahon Afirka, da tuni ta shafi mutane sama da miliyan 18 a fadin kasashen Habasha, da Somaliya da kuma Kenya.

Babban jami’in na MDD, ya bayyana haka ne, bayan kammala ziyarar kwanaki biyu a kasar Kenya ranar Juma'ar da ta gabata, inda ya gane wa idonsa mummunan tasirin kamfar ruwan sama na tsawon damina hudu a jere a yankin kahon Afirka, inda ya yi kira da a gaggauta kawo karshen wannan matsala, don ceto rayuka da al'umma sanadiyar tsanancin farin da ake fuskanta.

MDD ta ce, ya zuwa yanzu, matsalar fari a yankin kahon Afirka ta riga ta shafi mutane fiye da miliyan 18 a fadin kasashen Habasha, da Somaliya da Kenya, ciki har da a kalla mutane miliyan 16.7 da ke kwana da yunwa a kowace rana, kuma ba su san inda za su ci abinci na gaba ba.

A cewar MDD, da alamun wadannan alkaluma za su iya karuwa nan da makonni masu zuwa, ganin yadda lokacin damina wanda galibi ya kan fara daga Maris zuwa Mayu, amma bai kai matsakaici, wanda hakan ya zama fari mafi tsawo da aka fuskanta a yankin kusurwar Afirka a kalla shekaru arba'in. (Ibrahim)