Bayan Wani Mahaukacin Dan Bindiga Sai Mahaukaciyar Kasa
2022-05-16 16:17:22 CMG Hausa
A yayin da mutane suka je kasuwa don sayen kayayyaki a karshen mako, ba su san hawa ba balle sauke, sai kawai aka harbe su da bindiga. Wannan harin da ya abku ba gaira ba dalili shi ne abin da ake kira “hauka”.
Wani saurayi farar fata mai shekaru 18 a duniya ne, ya kaddamar da wannan hari a ranar Asabar da ta wuce, a wata kasuwar zamani dake garin Buffalo na jihar New York ta kasar Amurka. Inda ya rika watsa hotunan bidiyon yadda yake kashe mutane kai tsaye a shafin yanar gizo. Cikin ‘yan mintuna aka ga wasu mutane 13 sun fadi kasa. Cikinsu 10 sun mutu, wadanda dukkansu bakaken fata ne.
Kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun ce, saurayin ya sanya tambari mai siffar “bakar rana” a jikin rigarsa, wanda ya kasance alamar ‘yan Nazi, kuma irin tambarin da sojojin bataliyar Azov ta kasar Ukraine suka sanya. Ban da wannan kuma saurayin ya watsa wata doguwar sanarwa mai shafuka 180 a shafin yanar gizo, inda ya ce bakaken fata “ ba mutane ba ne”. Maganar dake nuna ra’ayin fararen fata masu tsattsauran ra’ayi.
Wannan tunani ne na mahaukata, amma ruwa ba ya tsami banza. Tun tuni kasar Amurka ta fara nuna goyon baya ga kungiyoyin kasar Ukraine masu adawa da kasar Rasha, ciki har da bataliyar Azov, mai akidar Nazi da ra’ayi na fararen fata sun fi sauran al’ummun duniya. Sai dai munafuncin dodo ya kan ci mai shi, yanzu kasar Amurka ita ma ta fuskanci akidar ‘yan Nazi, kana ra’ayi na nuna bambancin launin fata ya haddasa dimbin matsaloli a kasar.
Sai dai kasar Amurka ba ta lura da matsalolin sosai ba. Ko da yake bambancin launin fata da kabilanci sun haddasa hasarorin rayuka masu tarin yawa a kasar, kana yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha ya yi tasiri kan tsarin samar da kayayyaki na kasar Amurka, da haddasa matsalolin tattalin arziki, kamar karancin garin madaran jarirai a kasar. Ban da wannan kuma, wasu kwararru sun ce dimbin makamai da kasar Amurka ta ba kasar Ukraine a matsayin tallafi, za su iya shiga hannun ‘yan ta’adda, da haddasa rigingimu a duniya. Duk da haka, kasar Amurka na ci gaba da kokarin samar da makamai ga kasar Ukraine, kana tana shirin zartas da kudurin samar da karin tallafi da darajarsa ta kai dala biliyan 40 ga kasar Ukraine. Hakika kasar Amurka ba ta son ganin kura ta lafa a kasar Ukraine, ko da yake yakin da ake yi a can, ba zai haifar da da mai ido ga daukacin al’ummar duniya ba.
Hakan na nuna mana cewa, manufofin kasar Amurka sun sa aka samu wannan mahaukacin dan bindiga farar fata. Hakika, ita ma mahaukaciya ce, wato kasar Amurka. (Bello Wang)