logo

HAUSA

Adadin yarjejeniyoyin ciniki maras shinge da Sin ta daddale cikin shekaru goma ya karu da ninki daya

2022-05-16 11:12:30 CMG Hausa

Alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, adadin yarjejeniyoyin ciniki maras shinge da kasar Sin ta daddale ya karu da ninki daya, idan aka kwatanta da na shekarar 2012 wato shekaru goma da suka gabata.

Bayanai na cewa, daga shekarar 2012 zuwa wannan lokaci, kasar Sin ta daddale sabbin yarjejeniyoyin ciniki maras shinge 9 da kasashen ketare, inda hajojin da ba za a biya harajin kwastam suka kai kaso 90 bisa dari, a sa’i daya kuma, saurin aikin hukumar kwastam ta kasar, ya karu matuka.

A bangaren cinikin samar da hidima, kasar Sin ta yi alkawari a lokacin da ta shiga kungiyar ciniki ta duniya cewa, za ta bude sassa 100 ga kasashen ketare, yanzu haka ta kara sassa 22 yayin da ta daddale yarjejeniyar RCEP a farkon bana. Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin kuma mataimakin wakilin tattaunawa kan cinikin kasa da kasa Wang Shoucheng ya bayyana cewa, a cikin sassan da kasar Sin ta budewa ketare, 37 dake cikinsu sun daga matsayin bude kofarsu bisa yarjejeniyar RCEP. A bangaren zuba jari kuwa, kasar Sin ta yi alkawari cewa, za ta kara bude kofa a fannonin sana’ar kere-kere, da aikin gona, da hakar ma’adinai da sauransu.

Jami’in ya kara da cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari domin shiga yarjejeniyar CPTPP da ta DEPA. (Jamila)