logo

HAUSA

’Yan bindiga sun sace mutane 5 tare da kashe mutum 1 a arewacin Kamaru

2022-05-16 10:49:39 CMG Hausa

Majiyoyin tsaro a Kamaru sun ce, a kalla mutane 5 aka sace, yayin da aka kashe mutum 1 a yankin arewacin kasar.

Majiyar ta bayyana cewa, ’yan bindiga sun farwa kauyen Siri dake yankin Touboro na arewacin kasar da safiyar jiya Lahadi, inda suka sace mutane 5 da kashe wani mutum mai shekaru 54 da ya ki bin su.

Kafafen yada labarai na kasar sun ce wadanda aka sace sun hada da yara 3 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 12, da mace guda da kuma wani mutum mai shekaru 38.

An sace mutanen ne kasa da sa’o’i 10 da sace wata mata da jaririyarta tare da wata yarinya, a kauyen Ladde na yankin.

Rahotannin tsaro sun bayyana yankin Touboro a matsayin wurin da aka fi samun matsalar sace-sacen mutane cikin watan da ya gabata. (Fa’iza Mustapha)