logo

HAUSA

Mali ta fice daga G5 Sahel

2022-05-16 15:47:28 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Mali ta sanar a jiya Lahadi cewa, za ta janye daga dukkan sassa da hukumomin kungiyar G5 Sahel, ciki har da rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ayyukan ta'addanci.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin Mali Abdoulaye Maiga ya sanyawa hannu, shugabannin kungiyar sun yanke shawarar gudanar da zaman da aka saba yi karo na 8 a watan Fabrairun 2022 a Bamako, babban birnin kasar Mali, zaman da ya kamata ya kasance fara shugabancin karba-karba na kungiyar ta Mali.

Sai dai a cewar gwamnatin Mali, har yanzu ba a gudanar da zaman ba, wanda hakan keta shawarar da kungiyar ta yanke ne da kuma ainihin ka’idojin dake kunshe cikin kungiyar G5 Sahel. (Ibrahim)