logo

HAUSA

Idan amarya ba ta hau doki ba, bai kamata a dora mata kaya ba

2022-05-16 16:05:38 CMG Hausa

Ko shakka babu, duniyar bil adama tana fama da tarin kalubaloli wadanda ke zama barazana ga zaman lafiya, da tsaro, da walwala, har ma da ci gaban duniyarmu baki daya. Musamman idan muka yi la’akari da yadda duniyarmu ke fuskantar tarin matsaloli, kamar matsalar karayar tattalin arzkin sassa daban-daban na duniya, da matsalar sauyin yanayi wanda ke kara jefa rayuwar dan adam da sauran halittu gami da shi kansa muhallin halittun cikin garari, ga kuma matsalar annobar COVID-19 da ake fama da ita, sannan uwa uba ga matsalar yawaitar tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na duniya. Sai dai abin takaici ne, yayin da wata kasa ke yin bakin kokarinta wajen bada gagarumar gudunmawa domin ceto rayuwar bil adama daga cikin mawuyacin hali, amma wasu kasashen suna rufe idanunsu suna mantawa da dukkan alkhairan da wata kasa ke yi wajen kyautata rayuwar bil adama.

Alal misali, yayin da kasar Sin ke cigaba da kokarin neman kyautata rayuwar al’ummarta har ma da sauran al’ummun duniya baki daya, don samar da kyakkyawar makomar bil adama, amma wasu kasashen yamma na kokarin siyasantar da dukkan kokarin da kasar Sin ke yi na kyautata rayuwar dan adama. A baya bayan nan, kwararru masanan kasar Sin sun soki lamirin ’yan siyasar kasar Amurka masu adawa da ci gaban kasar Sin, wadanda ke shirya makarkashiya da makirci domin hana al’ummar yankin Xinjiang damamamkinsu na cigaba ta hanyar yada karairayin cewa, wai ana tilasta aikin kwadago a shiyyar. Masanan dai sun yi Allah wadai da wannan aniyar Amurkawan masu fakewa da siyasa.

Cao Wei, wani malamin jami’ar Lanzhou, ya bayyana cewa, wasu kamfanoni na fargabar kakkaba takunkumi daga kasar Amurka, hakan ya sa wasu daga cikin kamfanoni ba su son daukar ma’aikatan kwadago ’yan kabilan Uygur, inda hakan ke haifar da karuwar rashin ayyuka yi da kuma haifar da koma bayan ci gaban yanayin zaman rayuwar al’ummar Uygur.

Shi ma Ildos Murat, mataimakin shugaban tarayyar kungiyoyin ’yan kasuwan yankin Xinjiang, ya bayyana cewa, gaskiyar magana shi ne, Amurka ita ce kasar da har yanzu ayyukan kwadago na tilas ke cigaba da wanzuwa har a wannan karni na 21, yayin da ’yan ci rani su ne matsalar ta fi shafa, kuma gwamnatin Amurka ta kawar da kanta daga sauke hakikanin nauyin dake wuyanta wajen ba su kariya.

Ko shakka babu, za mu iya cewa, kokarin da kasar Sin ke yi wajen kyautata rayuwar al’ummun yankin Xinjiang, da sauran sassan kasar, har ma da sauran kasashen duniya, masamman kasashe masu tasowa, abin a yaba mata ne, kuma “idan amarya ba ta hau doki ba, bai kamata a dora mata kaya ba.” (Ahmad Fagam)