logo

HAUSA

Annobar COVID-19 ba za ta hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata ba

2022-05-16 21:52:39 CMG Hausa

Tarukan manema labarai biyu da gwamnatin kasar Sin ta shirya da safiyar yau Litinin sun jawo hankali matuka daga bangarori daban-daban.

Taro na farko, wanda hukumar kididdiga ta kasar Sin ta shirya, ya fitar da wasu muhimman alkaluman tattalin arzikin kasar a watan Afrilun bana. Duba da yadda halin da ake ciki a duniya ke canjawa, gami da yanayin annobar COVID-19 a cikin gida, tattalin arzikin kasar Sin na kara fuskantar matsin lamba, inda kakakin hukumar ya yi nuni da cewa, dalilin kuwa shi ne tasirin da annobar ta haifar na gajeren lokaci, amma ba zai hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata ba.

Taro na daban, wanda gwamnatin birnin Shanghai ta shirya kan dakile yaduwar cutar COVID-19 ya sanar da cewa, daga cikin yankuna 16 na birnin, akwai guda 15, wadanda aka riga aka yi nasarar hana yaduwar cutar tsakanin al’umma, kana tun daga watan Yunin bana, za’a farfado da harkoki da rayuwar yau da kullum a birnin. Bugu da kari, an kusan kawo karshen yaduwar cutar a lardin Jilin dake arewacin kasar Sin, a yayin da kura ta fara lafawa a lardunan Henan da Jiangsu da kuma Zhejiang. Duk wadannan al’amuran sun shaida cewa, manufar gwamnatin kasar Sin ta taka rawa, wato dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta, abun da ya samar da tabbaci ga farfadowar tattalin arzikin kasa.

Maida rayuwa gami da lafiyar dan Adam a gaban komai, babban tushe ne na aikin dakile yaduwar cutar a kasar Sin. Duk da cewa matakan kandagarkin cutar za su iya haifar da tasiri na gajeren lokaci ga rayuwar mutane a wasu sassa, amma shaidu sun nuna cewa, muddin an hana yaduwar cutar, za’a iya kirkiro kyakkyawan sharadi ga ci gaban tattalin arziki. (Murtala Zhang)