logo

HAUSA

Al’ummar Afirka Ba Su Bukatar A Yi Musu Lacca

2022-05-15 21:52:17 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei


Ta hanyar amfani da tashoshin sadarwa na wayoyin salula da manhajojin waya da yanar gizo da dai sauransu, bisa fasahohinta na zamani, Amurka ta dade da yi wa gwamnatocin kasa da kasa da kamfanoninsu da ma al’ummarsu leken asiri, ciki har da kasashen Afirka, muna iya cewa, ta amsa sunanta na babbar barauniyar satar bayanai.

Sai dai a kwanan nan, barauniyar ce take sake yin kiran a kama barawo, inda mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Wendy Sherman a ziyararta a nahiyar Afirka, ta ce wai, yadda wasu kasashen Afirka suka zabi kamfanin Huawei na kasar Sin a matsayin kamfanin dake samar musu hidimar sadarwa, na nufin sun yi watsi da ikon mulkin kasashensu.

Lallai, kasar da ta saba da sata tana kuma zaton sauran kasashen ma barayi ne. Domin neman lalata huldar da ke tsakanin Sin da Afirka, Amurka ta sha gurbata gaskiya tare da shafa wa kasar Sin bakin fenti.

Sinawa kan ce, “Sai wanda ya sa takalma ne ya san ko sun dace.” Jama’ar Afirka sun san wace ce aminiyarsu, ba su bukatar a yi musu lacca game da wanda ya kamata su yi hadin gwiwa. Shawarar da za mu ba Amurka ita ce, ta ba da hakikanin taimako ga kasashen Afirka don samun ci gabansu. (Mai Zane:Mustapha Bulama)