logo

HAUSA

Dakarun tsaron shiyya na hadin gwiwa sun kashe akalla mayakan Boko Haram 300 a tafkin Chadi

2022-05-15 17:23:00 CMG Hausa

A kalla mayakan kungiyar masu tsattsauran ra’ayi na Boko Haram 300 ne aka kashe yayin kaddamar da hare-haren dakarun wanzar da tsaron shiyya na hadin gwiwa wato MNJTF a yankunan tafkin Chadi, kamar yadda kakakin rundunar ya bayyana a ranar Asabar.

A sanarwar da aka fitar a birnin Maiduguri, dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, Kamarudeen Adegoke, kakakin rundunar tsaron MNJTF, yace an kashe mayakan ‘yan ta’addan ne a wasu hare-hare da aka kaddamar sau 30 a makonnin baya bayan nan da suka gabata, kuma a halin yanzu, rundunar wanzar da tsaron tana nazartar nasarorin da ta samu a farmakin da ta kaddamar kawo yanzu, domin daukar matakai na gaba.

Adegoke yace, sun lura kungiyar tana kara dogaro ne kan amfani da abubuwan fashewa wato IED, don haka sun yi kyakkyawan tanadi domin tinkarar ‘yan ta’addan.

Ya ce kimanin ma’aikatun sarrafa abubuwan fashewa hudu dakarun tsaron suka lalata kawo yanzu.

Adegoke ya cigaba da cewa, sama da mayakan ‘yan ta’addan da iyalansu 52,000 ne suka mika wuya ga dakarun MNJTF a yankunan da suka kaddamar da farmakin.

Sannan kimanin dakarun tsaron MNJTF shida da mamban rundunar tsaron sa kai ta fararen hula guda dake hadin gwiwa da sojojin ne suka mutu a yayin gudanar da ayyukan farmakin, sannan da dama daga cikin sojojin sun samu raunuka amma suna samun lafiya sannu a hankali.(Ahmad)