logo

HAUSA

Babban Titin Da Sin Ta Gina Zai Bunkasa Bangaren Yawon Bude Ido A Kenya

2022-05-14 16:28:30 CMG HAUSA

Ana sa ran babban titin da kasar Sin ta gina a kasar Kenya, zai bunkasa bangaren yawon bude ido na kasar.

Sakataren ma’aikatar kula da yawon bude ido da namun daji na kasar, Najib Balala ne ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Nairobi, babban birnin kasar, yana mai cewa, ana sa ran motoci za su fara gwada titin daga yau Asabar.

Ya kara da cewa, wannan wata makoma ce mai haske ga bangaren yawon bude ido na kasar, saboda ana sa ran babban titin na Nairobi zai rage lokacin da ake dauka daga filin jirgin sama zuwa wuraren yawon bude ido daban-daban dake fadin kasar.

Ya ci gaba da cewa, sun lura masu yawon shakatawa na fuskantar jinkirin tafiya tsakanin filin jirgin saman kasa da kasa na Jomo Kenyatta da cibiyar hada-hadar kasuwanci ta birnin. Amma da wannan babban titi, minti goma kacal ababen hawa za su dauka daga bangaren masu sauka a filin jirgin, zuwa cibiyar birnin, maimakon sama da sa’o’i 2 da suke dauka a yanzu.

Karkashin wani hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanin gine-gine na China Road and Bridge Corporation ne aka samar da kudin ginin babban titin mai tsawon kilomita 27.1 da ya hada da hannu biyu da kuma hannu 6. (Fa’iza Mustapha)