logo

HAUSA

Amurka Ba Ta Cimma Burinta A Asiya Ba

2022-05-14 20:32:49 CMG HAUSA

Ranar 13 ga wata, aka rufe taron koli na musamman tsakanin kasar Amurka da kasashe mambobin kungiyar ASEAN a birnin Washington, babban birnin kasar, wanda aka dakatar da kira a baya. Sai dai babu wani abu takamaimai cikin sanarwar hadin gwiwa da aka bayar bayan rufe taron. Manazarta sun yi nuni da cewa, lamarin bai wuce zaton mutane ba, wato Amurka ta yi shelar kara yin abota da kasashen Asiya, amma hakika dai tana yunkurin hada hannu ne da wadanda ke adawa da kasar Sin.

Kafofin yada labaru na kasashen duniya sun lura da cewa, Amurka ta yi alkawarin zuba wa kungiyar ASEAN dalar Amurka miliyan 150 a wannan karo. Amma akwai kasashe mambobi guda 10 cikin kungiyar ta ASEAN, don haka kudin da ko wace kasa za ta samu ba shi da yawa sam. Haka kuma a ‘yan kwanakin baya, majalisar wakilan Amurka ta zartas da shirin dokar tallafawa kasar Ukraine da ke shafar dalar Amurka biliyan 40. Kasashe mambobin kungiyar ta ASEAN sun kara fahimtar matsayinsu a wajen Amurka. Amurka ba za ta iya lallashinsu ba.

Har kullum kungiyar ta ASEAN na tsayawa tsayin daka kan kiyaye ‘yancin kansu da kuma tafiyar da harkokinsu da kansu. Sun san nufin Amurka na shirya wannan taron koli sosai. Ferdinand Romualdez Marcos, shugaba mai ci na kasar Philippines ya bayyana a fili cewa, kasarsa ba za ta kulla kawance da manyan kasashe ba, za ta tsara manufofinta na jakadanci da kanta.

Wannan shi ne dalili da ya sa tsarin tattalin arziki na tekun Indiya, da tekun Pasifik da Asiya da Amurka ta gabatar, bai samu amincewa tsakanin kasashe mambobin kungiyar ASEAN ba. Har ma kafofin yada labaru na Amurka sun ce, babu wani abu takamaimai da tsarin ya kunsa, inda suka bayyana shi a matsayinsa wata manufa maras amfani. (Tasallah Yuan)