logo

HAUSA

Nijeriya za ta sa ido kan masu furta kalaman kiyayya gabanin manyan zabukan kasa na shekarar 2023

2022-05-14 16:00:53 CMG HAUSA

 

Mashawarcin shugaban kasar Nijeriya kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya ce jami’an tsaron kasar na cikin shirin ko-ta-kwana, na tabbatar da cafkewa da gurfanar da mutanen da suke furta kalaman kiyayya yayin da babban zaben kasar ke karatowa a badi.

Da yake jawabi yayin wani taro da hukumar zabe ta kasar ta shirya a Abuja, babban birnin Nijeriyar, Babagana Monguno ya ce an bukaci shugabannin hukumomin tsaro, su kafa wani tsarin bibiya da gano ‘yan siyasar da ke da niyyar yiwa tsarin zaben kasar makarkashiya.

Haka zalika, ya ce za a sa ido kan ‘yan bangar siyasa da masu daukar nauyinsu, da zummar cafkewa da kuma gurfanar da su gaban kuliya.

A badi ne za a gudanar da babban zaben kasar dake da tarin ‘yan takara daga jami’iyyar APC mai mulki da tarin sauran jam’iyyun adawa, ciki har da PDP.

A nasa bangare, shugaban hukumar zaben kasar Mahmood Yakubu, ya ce yanayin tsaro a kasar da tasirinsa kan zabe, abun damuwa ne ga hukumar, yana mai alkawarin hukumar za ta ci gaba da hada hannu da hukumomin tsaro wajen tabbatar da nasarar gudanar dukkan shirye-shiryen da suka shafi zabukan dake karatowa. (Fa’iza Mustapha)