logo

HAUSA

Hajojin Habasha dake shiga kasar Sin na karuwa in ji jakadan Sin a kasar

2022-05-13 13:51:02 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Habasha Zhao Zhiyuan ya ce, adadin hajojin kasar Habasha da ake fitar zuwa Sin na karuwa, a gabar da hada hadar cinikayya, da hadin gwiwar zuba jari ke kara habaka tsakanin kasashen biyu.

A shekarar 2021, idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, adadin hajojin Habasha da aka shigar kasar Sin sun karu da kaso 8 bisa dari, yayin da sabbin jarin kai tsaye ko FDI da kamfanonin Sin suka shigar Habashan ya karu, da kaso 346 bisa dari.

Jakada Zhao ya yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamis, yayin taron tattauna batutuwa da suka shafi hada hadar zuba jari, da hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Habasha, wanda ofishin jakadancin Sin a Habasha, da hukumar kula da harkokin zuba jari ta Habasha ko EIC, da sashen bunkasa zuba jari na ma’aikatar kasuwanci ta Sin suka shirya a birnin Addis Ababa.

Jakada Zhao ya ce cikin jerin shekarun baya bayan nan, Sin ta zama babbar abokiyar cinikayyar Habasha, kuma kasar dake kan gaba wajen zuwa sabbin jarin kai tsaye na FDI a kasar, yayin da kasashen biyu ke kara zurfafa hadin gwiwa, karkashin shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya”.

Yayin taron, an sanya hannu kan takardar fahimtar juna mai nasaba da hadin gwiwar zuba jari tsakanin kasashen biyu, matakin da ya kasance sabo a fannin karfafa manufarsu ta bunkasa hadin gwiwar zuba jari, da shigar da sabon karfi ta fuskar hadin gwiwar sassan biyu.

A nasa bangare, mataimakin firaministan kasar Habasha, kuma ministan wajen kasar Demeke Mekonnen, ya jaddada cewa, kasarsa dake gabashin Afirka, ta zamo a sahun gaba, wajen karbar jarin kai tsaye daga kasashen waje, cikin sauran kasashen Afirka, yayin da Sin ke kara ingiza ikon kasar na cimma nasarori a wannan fage.    (Saminu)