logo

HAUSA

Cibiyar AFC za ta samar da dala biliyan 2 domin tallafawa farfadowar tattalin arzikin Afirka

2022-05-13 10:08:52 CMG Hausa

Cibiyar hadin gwiwar samar da kudaden gina ababen more rayuwa ta Afirka ko AFC, ta kaddamar da shirin kashe kudi har dala biliyan 2, domin farfado da tattalin arzikin nahiyar Afirka.

AFC ta bayyana wannan shiri ne a jiya Alhamis, tana mai cewa, matakin na da muhimmanci, musamman a gabar da duniya ke fuskantar tarin matsaloli, da suka hada da annobar COVID-19, da kuma rikicin Rasha da Ukraine a baya bayan nan.

Cikin wata sanarwar da cibiyar mai helkwata a Najeriya ta fitar, ta ce za ta samar da rabin kudaden gudanar da ayyukan, kana sauran za su fito daga sauran cibiyoyi abokan huldarta, dake samar da kudaden gudanar da ayyukan bunkasa ci gaba.

Sanarwar ta ce bisa shirin na AFC, za a fitar da kudaden ne a matsayin rance ga zababbun bankunan kasuwanci, da bankunan samar da ci gaba na kasashe masu tasowa, da kuma manyan bankunan dake kasashen Afirka daban daban, inda za a yi amfani da su wajen samar da kudaden musaya da aka fi bukata, don aiwatar da hada hadar cinikayya, da sauran ayyukan raya tattalin arziki a sassa daban daban.

Wasu kasashen Afirka ne suka kafa cibiyar AFC a shekarar 2007, an kuma dora mata nauyin samar da mafita ga manyan matsalolin kamfar ababen more rayuwa a Afirka, da shawo kan yanayin gudanarwa mai cike da kalubale. (Saminu)