logo

HAUSA

Amurka tana matukar son ganin duniya ta fada cikin ringingimu

2022-05-13 12:02:37 CMG HAUSA

 

Amurka kasa ce mafi karfi wadda take da fuskoki da dama. A wani bangare ba ta lura da rayukan jama’arta, balle hakkin tilas dake bisa wuyanta da harkokin duniya. Maimakon haka, a wani bangare kuma ta kan samar da makamai masu dimbin yawa don tayar da ringingimu a sassan duniya daban daban.

Ran 10 ga wata bisa agogon wuri, majalisar wakilan Amurka ta zartas da wani shirin tallafawa Ukraine na dala biliyan 40, daga cikinsu akwai tallafin soja da ya kai dala biliyan 25. Amma ga sauran kasashen dake tsakiyar nahiyar Amurka, wadanda ke matukar bukatar tallafin bunkasuwa, har yanzu Amurka ba ta kebe kudin tallafi ko kadan ba bayan aka yi shekaru 4 ana cacar baki kawai.

A matsayinta na kasa mafi karfin arziki a cikin MDD, ba ta biya kudin gudanarwa na majalisar da yawansa ya kai dala biliyan 1, adadin da bai kai kaso daya cikin goma na tallafin da take baiwa Ukraine ba.

A watan Maris na bana, shugaban Amurka ya gabatar da tsarin kasafin kudi na shekarar 2023 ga majalisar gudanarwa, inda yawan kasafin kudin