logo

HAUSA

MOFA: Sin Da Amurka Na Iya Yin Huldar Abota Na Bai Daya

2022-05-13 20:00:24 CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai Jumma'ar nan cewa, a matsayinsu na kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasifik, kasashen Sin da Amurka za su iya yin huldar abokantaka na bai daya.

Zhao ya bayyana haka ne a lokacin da yake karin haske, kan wani taro na musamman da ya gudana tsakanin Amurka da kuma kungiyar kasashen dake yankin kudu maso gabashin Asiya (ASEAN), a birnin Washington a ranakun Alhamis da Jumma'a, don tunawa da cikin shekaru 45 da kulla huldar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

A yayin taron, Amurka ta sanar da wani kunshin shirin raya kasa ga kungiyar ta ASEAN na sama da dalar Amurka miliyan 150, wanda ya shafi samar da ababen more rayuwa, da tsaro da yaki da cutar COVID-19.

Da yake bayani kan raya dangantaka tsakanin kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik, Zhao ya ce muhimmin abu shi ne, a saurari bukatarsu ta kiyaye zaman lafiya, da zurfafa hadin gwiwa da neman samun ci gaba tare.

Kasar Sin da kungiyar ASEAN, ba sa yin abubuwa marasa amfani, ko kuma sa kaimi ga yin fito na fito da juna a tsakanin rukunoni. Yana mai cewa, kasar Sin tana maraba da duk wani shiri na hadin gwiwa da zai taimaka ga samun dauwamammen ci gaba mai dorewa, da wadata tare a yankin.(Ibrahim)