logo

HAUSA

Sin ta kara raya dangantakar abokantaka a tsakaninta da kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya”

2022-05-13 20:23:42 CMG Hausa

Daga ranar 14 zuwa 15 ga watan Mayu na shekarar 2017, an gudanar da taron tattaunawa kan hadin gwiwar kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na farko a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron tare da yin jawabi. Xi ya jaddada cewa, ya kamata a raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda za ta zama hanyar shimfida zaman lafiya, da samun wadata, da bude kofa ga kasashen waje, da yin kirkire-kirkire, da kuma mu’amalar al’adu.

A halin yanzu dai, an hada jama’ar kasashen dake cikin shawarar tare ta hanyar raya shawarar waje guda, kuma idan har raya shawarar ya kasance yin hadin gwiwa da samun moriyar juna da bunkasuwa tare, to hakan zai amfanawa jama’ar kasa da kasa. A ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 2021, bisa sa idon shugabannin kasashen Sin da Laos, an fara yin amfani da hanyar jirgin kasa a tsakanin Sin da Laos mai tsawon kilomita 1035, wanda aka gina cikin tsawon shekaru 5. Don haka, an cimma burin kasar Laos na hada ta da sauran kasashen duniya ta hanyar hanyar jirgin kasa.

Rahoton da bankin duniya ya fitar na nuna cewa, ya zuwa shekarar 2030, za a fitar da mutane miliyan 7 da dubu 600 daga talauci mai tsanani a duniya da kuma fitar da mutane miliyan 32 daga matsakaicin talauci ta hanyar raya shawarar “ziri daya da hanya daya”. Don haka, shawarar “ziri daya da hanya daya” za ta kasance muhimmiyar hanyar sa kaimi ga samun wadata tare. (Zainab)