An kafa kungiyar ba da ilimin sana’o’i ta Sin da Afrika
2022-05-13 15:21:03 CMG HAUSA
A ran 11 ga wata, kungiyar mu’ammala ta fuskar ba da ilimi ta kasar Sin, ta kira wani taro na ingiza shirin ba da ilimin sana’o’i tsakanin Sin da Afrika, kuma taron kafa kungiya a wannan fanni ta kafar bidiyo da a zahiri, don tabbatar da shawarwarin hadin kan Sin da Afrika, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika.
Mataimakin daraktan sashin hadin kan kasa da kasa, da yin mu’amala na hukumar ba da ilmi na Sin Jia Peng, ya taya murnar kafuwar kungiyar. Ya kuma ce makomar nahiyar Afrika ita ce matasa, kuma mafitar matasa ita ce samun ilimi.
Ya ce gwamnatin Sin ta dade tana dora matukar muhimmanci kan hadin kan bangarorin biyu a wannan fuska, musamman ma a fannin ba da ilimi na sana’a, abin dake da makoma mai haske wajen hadin kansu. Sin na fatan kafa tsari mai yakini da kasashen Afrika cikin dogon lokaci, don goyon bayan shiri mai taken “Makomar Afrika: hadin kan Sin da Afrika kan ba da ilmi na sana’a”, ta yadda za a horas da kwararru a fannin samar da kayayyaki da raya tattalin arziki na yanar gizo, da dai sauran sabbin sana’o’i. (Amina Xu)