logo

HAUSA

Kamaru: Ba wanda ya tsira daga hadarin jirgin sama

2022-05-13 10:10:37 CMG Hausa

Kafar watsa labarai ta CRTV dake kasar Kamaru, ta ce ba wanda ya tsira daga hadarin karamin jirgin saman fasinjan nan da ya rutsa da mutane 11, a wani daji dake yankin tsakiyar kasar.

A ranar Alhamis ne CRTV ta bayyana a shafinta na Tiwita, cewar bayan da aka yi aikin ceto da bincika a ranar Laraba, an gano tarkacen jirgin a sashen dajin “Upper Sanaga” na yankin Albert Nanga dake tsakiyar kasar.

A cewar wata sanarwar da kamfanin jigilar danyen mai na kasar Kamaru ya fitar, jirgin na dauke ne da ma’aikatan kamfanin, da suka kunshi fasinjoji 9 da matuka 2, ya kuma tashi ne daga birnin Yaounde, fadar mulkin kasar zuwa wata mahakar danyen mai dake Dompta a arewacin kasar, kafin daga bisani na’urorin bibiyar tafiyar jirage su daina jin duriyarsa.

Hadarin ya lakume rayukan dukkanin wadanda ke cikin jirgin, dake lura da wani bututun sinadarin “hydrocarbon”, wanda ya ratsa Kamaru zuwa kasar Chadi mai makwaftaka.

Wasu kafafen watsa labarai a kasar ta Kamaru, sun alakanta aukuwar hadarin da wata guguwa mai karfin gaske. (Saminu)