logo

HAUSA

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 3.4 a shekarar 2021

2022-05-12 12:30:28 CMG HAUSA

 

Najeriya ta samu bunkasar tattalin arikinta a shekarar 2021, inda ma’aunin GDPn kasar ya karu da kashi 3.4 bisa 100, lamarin dake alamta samun kyautatuwar yanayinsa bayan karayar tattalin arzikin da kasar ta fuskanta a shekarar 2020, kamar yadda rahoton da hukumar kididdigar kasar NBS ta fitar a ranar Laraba ya bayyana.

Rahoton baya bayan nan game da tattalin arzikin, wanda hukumar NBS ta fitar ya nuna cewa, tattalin arzikin Najeriya ya ci gaba da bunkasa a rubu’i na biyu na shekarar 2021, a yayin da hakikanin GDPn kasar ya karu da kashi 5.01 bisa 100.

A rubu’i na uku na shekarar 2021, GDPn ya karu da kashi 4.03 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2020, yayin da karuwar GDPn a rubu’i na hudu na shekarar 2021 ya kai kashi 3.98 bisa 100. Rahoton na NBS ya ce, karuwar hakikanin GDPn kasar na shekarar ya kai kashi 3.4 bisa 100 a shekarar 2021, idan an kwatanta da kashi 1.92 bisa 100 da aka samu a shekarar 2020, yayin da a shekarar 2019 tattalin arzikin kasar ya karu cikin yanayi mai kyau da kashi 2.27 bisa 100.

Rahoton ya ci gaba da cewa, kyakkyawan yanayin bunkasuwar tattalin arzikin Najeriyar da aka samu a shekarar 2021, ana danganta shi da karuwar hada-hadar kayan masarufi na bukatun gida, yayin da hakikanin bukatun kayan masarufin na shekara guda ya kai kashi 25.65 bisa 100, idan an kwatanta da na shekarar 2020 wanda ya ragu da kashi 1.69 bisa 100 a shekarar 2020. (Ahmad)