logo

HAUSA

Gasar yada kanin wani kan babbar hanya da kasar Sin ta gina a Kenya za ta habaka fatan kasar na bunkasar tattalin arziki

2022-05-12 16:34:50 CMG Hausa

Charles Koskey, mai shekaru 29 da haihuwa na da otal da yake gudanarwa. Yana kuma cikin dandazon wadanda suka shiga gasar gudun yada kanin wani cikin nishadi, wanda aka gudanar albarkacin bikin kaddamar da babbar hanyar mota da kasar Sin Sin ta gina a birnin Nairobi na kasar ta Kenya a ranar Lahadin karshen mako.

Dan wasan gudun ajin da ba na kwararu ba, ya ce abun da ya sanya shi shiga wannan gasa shi ne imanin sa da cewa, babbar hanyar ta zamani mai tsawon kilomita 27.1, wadda kuma za ta hade manyan sannan birnin, za ta ba da babbar gudummawa wajen kara raya harkar sufuri, da hade sassa daban daban da bunkasa cinikayya.

Koskey wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin wata zantawa, ya ce "Da zarar an bude wannan hanya ga motoci, muna fatan samun sassaucin cinkoson ababen hawa a birnin Nairobi, tare da sanya birnin zama mai kayatarwa da jan hankalin masu zuba jari".

Koskey ya kammala gudun rabin zango ko “half-marathon” kan babbar hanyar ta Nairobi, gasar da ma’aikatar wasanni ta Kenya ta shirya, gabanin baiwa ababen hawa damar fara amfani da titin daga ranar 14 ga watan Mayun nan.

Dandazon masu gudu ajin da ba na kwararru ba sama da 10,000, da ma kwararrun ‘yan wasan tsere sun shiga an fafata da su a gasar da aka yiwa lakabi da “Uhuru Classics”. An kuma kasa gasar gida 4, wato ajin tseren kilomita 10, da na kilomita 5, da na kilomita 21, da kuma na dogon zangon kilomita 42.

Koskey ya ce wannan gasa ta tsere ta daga darajar wannan babbar hanya, wadda za ta ba da hidimar rage lokacin sufuri tsakanin yammacin birnin Nairobi zuwa sashen babban filin jirgin saman kasar dake kudanci, daga sa’oi 2 zuwa kimanin mintuna 20 kacal.

A cewar Koskey, "Wannan aikin more rayuwa ne mai muhimmanci ga kasa. Zai samar da kyakkyawan yanayi mai ban sha’awa ga birnin Nairobi, kuma masu ziyartar birnin za su ji dadin zirga zirga zuwa filin jirgin sama".

Koskey, ya kara da cewa, tuni babbar hanyar ta haifarwa birnin Nairobi riba ta fuskar daga matsayin sa na zama birni mai jan hankalin karin ‘yan kasuwa, da hada hadar sufuri da harkokin shige da fice.

Babbar hanyar wadda kasar Sin ta gina karkashin shirin gina hanyoyi da gadoji da hadin gwiwar gwamnatin kasar Kenya, za ta bude sabon babin sauya yanayin sufuri a birnin Nairobi fadar mulkin Kenya.

Yayin gabatar da lambobin yabo, bayan kammala gasar tseren, shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya ce ginin babbar hanyar na cikin babban shirin gwamnatin sa na zamanintar da birnin mafi girma a gabashin Afirka.

Shugaba Kenyatta ya kara da cewa, "Sakamakon ci gaban ayyukan zamanantar da ababen more rayuwa, kamar babbar hanyar ta Nairobi, kasar za ta ci gajiya mai yawa ta fuskar saukaka sufuri, da ingantuwar cinikayya, da bunkasa zuba jari, da samar da kyakkyawan muhallin kiwon lafiya”.

Ya kara da cewa, a ranar 14 ga watan nan na Mayu, za a bude babbar hanyar a matakin gwaji, kuma ana fatan hanyar za ta ba da damar samar da karin ayyukan yi, da bunkasa harkokin yawon shakatawa, da fannin sarrafa hajoji, da sauran hidimomin hada hadar kudade.

A nata bangaren, sakatariyar harkokin wasanni a majalissar gudanarwar kasar Kenya Amina Mohamed, cewa ta yi wannan babbar hanya ta birnin Nairobi, wadda ta cika dukkanin sharuddan karbar bakuncin gasannin tsere mai dogon zango, za ta bunkasa harkokin yawon shakatawa masu nasaba da wasanni a kasar.

Ta ce "Mun samu dama ta karbar bakuncin manyan ‘yan wasannin motsa jiki, da gasannin kasa da kasa da za a iya gudanarwa nan gaba a wannan babbar hanya. Hakan zai ingiza matsayin kasar Kenya na kasancewa cibiyar gudanar da manyan gasannin tsere".

Shi kuwa Brimin Misoi, mai shekaru 32 da haihuwa, wanda ya lashe gasar gudun yada kanin wani ta dogon zango, cewa ya yi ya yi matukar farin ciki da bin wannan babbar hanya ta Nairobi, yana mai cewa, tuni Kenya ta cancanci samun irin wadannan ababen more rayuwa na zamani.

Misoi, wanda dan asalin gundumar Elgeyo Marakwet ta arewa maso yammacin Kenya ne, yankin da ake wa lakabi da “Yankin masu cimma nasara” ya kara da cewa, za a samu alfanu ta fuskar zamantakewa da raya tattalin arziki, daga bude wannan babbar hanya wanda zai karade dukkanin sassan kasar.

A nasa bangare kuwa, ma’ajin kungiyar ‘yan wasan motsa jiki ta yankin kudancin kasar Stephen Ole Marai, cewa ya yi kasancewar babbar hanyar ta hade filin jiragen sama zuwa yankuna mafiya cunkoson jama’a, za ta share fagen saukaka gudanar da hada hadar kasuwanci, da janyo baki masu yawon bude ido, tare da baiwa ‘yan wasan motsa jiki na Kenya damar shiga kasashen ketare domin fafatawa a manyan gasanni.

Wannan babbar hanya da aka gina a birnin Nairobin kasar Kenya, ta samar da guraben ayyukan yi masu dinbin yawa ga al’ummun wurin, da kuma kudaden shiga ga masu kwangilar kayayyakin gini da aka yi amfani da su wajen gudanar da ita.