logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Slovenia sun yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar jakadanci

2022-05-12 20:33:11 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Slovenia Borut Pahor, suka yi musayar sakonnin taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru 30 da suka gabata, kasashen Sin da Slovenia, suna mutunta juna da nuna daidaito, sun kuma samu sakamako mai kyau a hadin gwiwa mai moriyar juna, sun kuma shaida karuwar musayar al'adu da al’ummu, lamarin da ya yi matukar amfanar da jama'ar kasashen biyu.

Ya ce, a yayin da ake fuskantar annobar COVID-19 kuwa, jama'ar kasashen biyu sun nuna goyon baya ga juna, da ma nuna zumunci mai karfi tsakanin kasashen Sin da Slovenia.(Ibrahim)