logo

HAUSA

Sin ta kafa tarihin cimma manyan nasarori a fannin bude kofa ga waje

2022-05-12 15:02:27 CMG HAUSA

 

Jami’an ma’aikatar kasuwancin kasar Sin sun yi karin haske game da irin nasarorin da Sin ta cimma, a fannin bude kofa ga kasashen waje, wanda hakan ya sanya kasar kafa wani muhimmin tarihi a wannan fanni.

Jami’an sun bayyana hakan ne yayin wasu tarukan ’yan jaridu da suka gudana a yau Alhamis, wadanda aka yiwa lakabi da "Shekaru 10 na Sin”. Jami’an sun ce cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta yi namijin kokari wajen yayata manufarta ta bude kofa ga waje, inda kuma ta cimma manyan nasarori.

A shekarar 2012, jimillar cinikayyar kayayyaki, da hidimomi na Sin ta kai darajar dalar Amurka tiriliyan 4.4, adadin da shi ne na 2 mafi girma a duniya a lokacin. Yayin da a shekarar 2021 kuma, wannan adadi ya karu zuwa dalar Amurka tiriliyan 6.9, adadin da ya zamo na farko a duniya cikin shekaru 2 a jere.

Kari kan hakan, Sin ta samar da kyakkyawan muhallin zuwa jarin ta a waje, baya ga baiwa sassan duniya damar zuba jari a yankunan ta.

Tun daga shekarar 2017, Sin ke matsayi na 2 a duniya wajen janyo jarin waje cikin shekaru 4 a jere. Adadin jarin da Sin ke zuwa ga kasashen waje shi ma na cikin jerin na kasashe 3 dake sahun gaba a duniya, kuma shawarar Sin ta "Ziri daya da Hanya daya" mai kunshe da manufofin raya tattalin arziki da cinikayya na kara fadada bisa inganci. (Saminu)