logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kan sa game da kisan ’yar jaridar Al Jazeera

2022-05-12 13:54:12 CMG HAUSA

 

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, kuma a bude, game da harbe ’yar jaridar kafar labarai ta Al Jazeera Shireen Abu Akleh.

Wata sanarwa da ofishin Mr. Guterres ya fitar ta ce, ana zargin sojojin Isra’ila da hare Abu Akleh mai shekaru 51 a duniya tana tsaka da aiki, a garin Jenin na yammacin kogin Jordan, wanda Isra’ila ta mamaye. 

Kaza lika an jikkata wani dan jaridar na Al Jazeera mai suna Ali al-Samudi, duk da cewa shi da abokiyar aikin nasa suna sanye da hular kwano, da rigar kariya mai dauke da shaidar cewa su ’yan jarida ne.

Guterres ya yi Allah wadai da kisa, ko kaiwa ’yan jarida farmaki. Yana mai cewa, ko kadan bai dace a muzguna musu, yayin da suke aiwatar da ayyukansu ba. Ya kuma jaddada bukatar gudanar da bincike mai zaman kansa, domin gano hakikanin dalilin farwa ’yan jaridar.  (Saminu)