logo

HAUSA

MDD ta yi gargadi game da karuwar masu fama da kamfar abinci a gabashin Afirka

2022-05-12 10:01:39 CMG HAUSA

 

MDD ta yi gargadin cewa, mai yiwuwa adadin mutanen dake fuskantar matsanancin karancin abinci, da ruwan sha a yankin gabashin Afirka, ya karu zuwa mutane miliyan 20.

Ofishin tsare-tsaren ayyukan jin kai na majalisar ko OCHA ya ce, ya zuwa yanzu, adadin masu fama da kamfar abinci a Habasha, da Kenya, da Somaliya, sun haura mutane miliyan 15.

Wata sanarwa da OCHA ya fitar a birnin Nairobin kasar Kenya ta ce a kasashen 3, akwai yara kanana kimanin miliyan 5.7 dake fama da tamowa, yayin da fari ya hallaka dabbobi sama da miliyan 3, wadanda kuma da su ne makiyayan yankunan ke samun abun dogaro.

An fitar da sanarwar ne kwanaki 2, gabanin ziyarar da sakataren ayyukan jin kai da samar da tallafi na MDD Martin Griffiths zai kai kasar ta Kenya.

Mr. Griffiths zai sauka a birnin Nairobi ne a yau Alhamis, da nufin janyo hankalin sassan kasa da kasa game da mummunan tasirin sauyin yanayi, wanda ke haifar da yanayin jin kai na gaggawa, da kuma bukatar zage damtse ga bunkasa matakan kare rayukan al’ummun yankin na gabashin Afirka kafin lokaci ya kure.   (Saminu)