logo

HAUSA

Kasar Sin na tallafawa gina “ganuwar bishiyoyi a Afirka”

2022-05-12 11:05:12 CMG Hausa

Yanzu haka, taron UNCCD COP15, wato taron masu ruwa da tsaki na yarjejeniyar hana kwararowar hamada ta MDD karo na 15, na gudana a birnin Abidjan, hedkwatar tattalin arziki ta kasar Cote d’Ivoire, taron da ke mai da hankali a kan samar da wani dauwamammen shiri na daidaita matsalar farfado da filayen kasa da ma yaki da fari.

Tun bayan da kasar Sin ta daddale yarjejeniyar hana kwararowar hamada ta MDD, har kullum tana kokarin sa kaimin aiwatar da yarjejeniyar, a yayin da kuma take hada kan kasashen Afirka wajen aiwatar da shirin gina “ganuwar bishiyoyi” a Afirka, don kare kwararowar hamada, shirin da ake kira “Great Green Wall” a Turance.

A ranar 13 ga watan Afrilun wannan shekara, an shirya kwas na tallafawa shirin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kuma jami’ai sama da 20 da suka zo daga kasashen Burkina Faso, da Chadi, da Mali, da Nijer, da Mauritania, da Senegal sun halarci kwas din ta yanar gizo.

A gun taron da ke gudana a wannan karo, kasar Sin ta gabatar da wasu shawarwari uku, ciki har da inganta hadin gwiwar kasa da kasa, da sa kaimin ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, sai kuma a inganta dokokin kasa da kasa, shawarwarin da suka kara samar da kuzari ga kokarin da ake yi na kiyaye muhallin nahiyar Afirka.

An dai kaddamar da taron a ranar 9 ga wata, kuma za a kammala shi a ranar 20 ga wata.  (Lubabatu)