logo

HAUSA

An kashe sojoji 8 da jikkata wasu 13 a harin ta’addanci a Togo

2022-05-12 10:02:10 CMG HAUSA

 Kimanin sojoji takwas aka hallaka, kana an raunata 13, a wani da ’yan bindigar da ba a tantance su ba suka kaddamar da sanyin safiyar ranar Laraba a arewacin kasar Togo, kusa da kan iyaka da kasar Burkina Faso, gwamnatin kasar ta bayyana cikin wata sanarwa.

Da misalin karfe 3 na safiyar ranar Laraba agogon wurin, wata tawagar dakarun tsaro masu yaki da ta’addanci dake yankin Kpendjal, a arewacin Togo, ta gamu da harin kwanton bauna daga ’yan ta’adda karkashin wata kungiyar da ba a tantance ba wadanda ke dauke da muggan makamai. A cewar sanarwar, harin ya yi sanadin kashe dakarun tsaro takwas da kuma raunata wasu 13.

Sanarwar ta ce, gwamnatin kasar Togo ta yi Allah wadai da kakkausar murya game da wannan harin da aka bayyana shi a matsayin na matsora, kana ta ba da tabbaci ga dukkan jama’ar kasar cewa, dakarun tsaron za su yi dukkan kokarinsu wajen tabbatar da tsaron kasar.

Kasar Togo ta hada kan iyaka da Burkina Faso ta bangaren arewaci, kasar ta yankin Sahel dake yammacin Afrika, ta jima tana fama da jerin hare-haren ta’addanci tun a shekarar 2015. (Ahmad)