logo

HAUSA

Soke kara biyan haraji ga kamfanonin Sin da Amurka ta yi ya dace da moriyar kamfanoni da masu sayayya na Amurka

2022-05-12 20:40:06 CMG Hausa

Ofishin wakiliyar cinikayya na kasar Amurka, ya sanar a kwanakin baya cewa, an fara sake bibiyar manufar kara kudin haraji ga kamfanonin Sin, ya ce, kasar Amurka tana nazari ko za a rage harajin da aka sanyawa kamfanonin Sin ko a’a.

Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, bisa yanayin tinkarar hauhawar farashin kaya na yanzu, soke kara biyan haraji ga kamfanonin Sin da Amurka ta yi, ya dace da moriyar kamfanoni da masu sayayya na kasar Amurka, kuma hakan zai amfanawa kasar Amurka, da kasar Sin, har ma da duniya baki daya. (Zainab)