logo

HAUSA

Duniya Na Bukatar Hadin Gwiwar Dakile Manyan Matsalolin Da Bil Adama Ke Fama Da Su

2022-05-12 16:14:28 CMG Hausa

Ko shakka babu, duniya na fuskantar manyan kalubale daban daban, musamman a shekarun baya bayan nan, rikicin Rasha da Ukraine, da matakan da wasu kasashen yamma ke dauka na bin ra’ayin kashin kai, da kakkaba takunkumi da wasu kasashen yamma ke yi ga wasu sassa, da tasirin sauyin yanayi, tare da cutar COVID-19 dake kara bazuwa a sassan kasashen duniya daban daban, dukkaninsu sun kara matsi ga tattalin arzikin duniya.

Masharhanta na ce, hauhawar farashin abinci, da makamashi, na ingiza kalubalen kamfar abinci da makamashi, ta yadda duniya ke tunkarar kamfar abinci mafi muni, tun bayan kalubalen kamfar abinci na shekarar 2007 zuwa 2008.

A nahiyar Afirka ga misali, farashin abinci ya ninka har sau 3 tun daga shekarar bara. Kaza lika su ma kasashen Turai da dama na fuskantar wannan kalubale, inda ma’aunin farashin kayayyakin masarufi ko CPI a wasu daga cikin su ya karu, da kusan kaso 18 zuwa 20 bisa dari.

Tuni dai MDD ta samar da tallafin abinci da darajarsa ta kai dala miliyan 97 ga kasashe 88, yayin da adadin ’yan gudun hijira ke karuwa sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.

Da yawa daga kasashen yamma, sun gaza sauke nauyin alkawuran da suka dauka a tsawon lokaci, wato kashe kaso 0.7 bisa dari na daukacin kudaden shigar su a fannin tallafin samar da ci gaba, manufar da tun da farko ke da nufin bunkasa ayyukan noma a kasashe masu tasowa, musamman na Afirka, da gabas ta tsakiya, ta yadda hakan zai wanzar da damar samar da isasshen abinci ga al’ummun kasashe masu tasowa.

Ko shakka babu, idan har ana da burin shawo kan wadannan matsaloli, ya zama wajibi gwamnatoci su goyi baya ga kiraye-kirayen MDD, na ingiza shigar da abinci, da takin zamani na kasashen Rasha da Belarus zuwa kasuwannin duniya, domin bunkasa samar da hatsi, da kaucewa karuwar matsalar kamfar abinci.

Tuni dai kasar Sin ta rungumi wannan manufa, inda a bangarenta, take dora muhimmanci ga tallafawa raya noma a kasashe masu tasowa. Sin tana kuma ci gaba da ingiza ci gaban ginshikan tattalin arzikin duniya baki daya.

A daya hannun kuma, tun bayan da kasar Sin din ta daddale yarjejeniyar hana kwararar hamada ta MDD, kawo yanzu tana kokarin bunkasa aiwatar da wannan yarjejeniyar tare da hadin gwiwar kasashen Afirka, inda take fatan cimma nasarar aiwatar da shirin gina “ganuwar bishiyoyi” ta Afirka, don kare kwararowar hamada, shirin da ake kira da “Great Green Wall”. Wannan ya zama wani mataki na ba da tabbaci ga burin da ake da shi na “A guda tare a tsira tare”. (Saminu Hassan)