logo

HAUSA

Koci Zhang ya zama tauraro a fannin horas da ‘yan makaranta masu buga kwallo

2022-05-11 15:21:27 CRI

A lardin Lanzhou dake kasar Sin, ana gudanar da gasannin kwallon kafa daban daban a makarantun sakandare, inda irin wadannan gasanni, da kuma daruruwan yara ‘yan makaranta dake kara shiga harkar kwallo suka ingiza koci Zhang Dehe, zuwa cimma burin sa na ba da gudummawa ga ci gaban wasan, tare da mayar da filayen wasannin irin wadannan makarantu, zama wurin kyankyashe Sinawa ‘yan kwallon kafa.

Koci Zhang mai shekaru 57 da haihuwa, koci ne a makarantar sakandare ta 2 dake gundumar Jingyuan, inda a nan ya jagoranci daliban da ya horas zuwa lashe gasar makarantun sakandare ta lardin Gansu dake arewa maso gabashin Sin. Cikin shekaru 34 da suka gabata, koci Zhang ya ci gaba da aiwatar da aikin sa cikin himma da kwazo.

Da yake tsokaci game da hakan, Zhang ya ce "Kusan ba kayan wasan kwallon kafa masu inganci a makarantar a lokacin da na zo, in banda wasu tsofaffin kwallayen kafa guda 3. In ban da su ba wasu sauran kayan wasa. Tawagar ‘yan wasan makarantar na samun sabbin kwallaye 4 ne kacal a duk shekara. Kuma idan sun lalace sai dai a gyara su a ci gaba da amfani da su".

A shekarar 1988, Zhang Dehe ya koma tsohuwar makarantar da ya kammala, a matsayin malamin koyar da motsa jiki, kuma kocin tawagar kwallon kafar makarantar.

Koci Zhang ya fara fuskantar kalubale, yayin da dalibai sama da 100 suka nemi shiga tawagar kwallon kafar makarantar wadda zai rika horaswa. Bayan ya zabi ‘yara dalibai 26 daga cikin su, sai kuma ya kira su fara yin horo da misalin karfe 6 na safe, amma kuma kusan rabin su ne kadai suka halarta.

Zhang ya ce "Iyayen yara da dama sun fi mayar da hankali ga karatun yaran su, suna kuma matukar adawa da baiwa yaran su damar shiga kungiyar kwallon kafa. Don haka sai na rika tara dukkanin daliban dake cikin tawagar kwallon kafar a wani aji guda, ina duba ci gaban kwazon su a makaranta a ko wane yammaci".

Zhang ya ce, ya kuma gana da iyayen su, da su kan su daliban, domin wayar da kan su, su sassauto daga ra’ayin kin wasan kwallo, ya kuma yi magana da malamai ‘yan uwan sa, da nufin su ma su ja hankalin dalibai zuwa ga ci gaba da kasancewa cikin tawagar kwallon kafar.

Ya ce "Kwallon kafa ba karin nauyi ne a wuyan ‘yan makaranta ba. Horon kwallon kafa, da shiga gasannin wasan na baiwa yara damar motsa jiki, baya ga karfafa musu zuciya da hakan ke yi, wajen kara dagewa har a kai ga cimma nasara, kana hakan na karfafa musu tunani a fannin yin wasu abubuwa tare da juna. Wadannan muhimman dabaru ne da ko wane matashi ke bukatar su yayin da yake tasowa".

A shekarar 1999, kwazon Zhang ya haifar da kyakkyawan sakamako, domin kuwa tawagar da yake horasawa ta lashe gasar kwallon kafa ta makarantun sakandare ta dukkanin lardin Gansu.

Bayan nan, sai tawagar Zhang ta ci gaba da shiga gasannin lardi daban daban, kuma cikin kankanin lokaci, sai dakin ajiye lambobin yabo na kungiyar kwallon kafar da yake horaswa ya cika da kofuna, da lambobin yabo masu tarin yawa.

Zhang ya cimma nasarar zama koci mafi hazaka, a matakin makarantun sakandare dake kasar Sin tsakanin shekarun 2004 zuwa 2013, inda hukumar kwallon kafar makarantun sakandare ta kasar Sin ta karrama shi. A shekarar 2020, an sanya sunan sa cikin masu horas da kwallon kafa mafiya kwarewa a matakin makarantun sakandaren kasar Sin.

Cikin shekaru 10 na baya bayan nan, makarantar sakandare ta 2, inda yake ba da horo, ta yaye kwararrun ‘yan kwallo 300 zuwa jami’oin koyar da wasanni daban daban dake kasar Sin, ciki har da jami’ar horas da wasanni ta Beijing, da jami’ar Lanzhou.

Zhang ya ce "Da yawa daga wadannan dalibai sun zama masu horaswa yanzu, kuma dukkanin su na tallafawa wajen raya kwallon kafa a makarantun kasar Sin".

Jia Yonggang, mai shekaru 46 da haihuwa, ya kammala makarantar sakandare ta 2, kuma a lokacin yana dalibta a makarantar, jigo ne a tawagar kwallon kafa da ta lashe gasar makarantu ta shekarar 1993. Shi ma Jia ya koma makarantar a shekarar 1996 a matsayin koci, bayan kammala karatun sa a jami’a.

Tun daga wannan lokaci ne kuma, Jia tare da wanda ya horas da shi, kuma abun koyinsa Zhang, suka hada hannu wajen ci gaba da horas da karin dalibai kwallon kafa a makarantar.

Jia ya ce dabarar mika fasaha daga zuri’a zuwa zuri’a na da matukar muhimmanci. A matsayin sa na kwararren koci a matakin makarantun kasar Sin. An zabi Jia domin halartar kwas din kara sanin makamar aiki a kasar Faransa a shekarar 2015. Cikin shekaru sama da 2 da suka gabata, makarantar sakandare mai lamba 2, ta yi hayar wani baturen kasar Argentina domin ya kara horas da tawagar ‘yan kwallon ta.

Zhang ya yi nuni da cewa, mayar da hankali ga harkar kwallon kafa ta makarantun sakandare yana da muhimmanci a fannin raya wasanni, da kuma karfafa kuzarin jikin dalibai, da ma fadada ilimin su ta fuskar wasanni a yayin da suke girma.

A shekarar 2020, kasar Sin ta haye adadin da ta tsara, na gina makarantun da za su maida hankali ga harkar wasan kwallon kafa har 20,000, kuma yawan yaran kasar dake shiga wasan kwallon kafa na ta karuwa sannu a hankali.