logo

HAUSA

Kamfanin Huawei ya baiwa matasan da suka kammala karatun jami’a a Habasha damammaki a fannin fasahohin zamani na ICT

2022-05-11 11:16:44 CMG Hausa

Sashen kamfanin Huawei na kasar Sin dake kasar Habasha ya shirya taron dandali da nufin baiwa sabbin daliban da suka kammala karatun jami’a damammakin samun horo a fannin fasahar sadarwa ta zamani.

Tamire Dawud, manajan sashen bunkasa fasahar ICT a kamfanin fasahar sadarwa na Huawei dake Habasha, ya ce kafa dandali, wani bangare ne na burin kamfanin Huawei na ci gaba da bada horo, da samar da ilmi, ga sabbin matasan da suka kammala karatun jami’a domin horar da su game da sabbin dabarun zamani na kamfanin, da suka hada da fannonin yada bayanai, da fasahar kwaikwayon tunanin dan adam wato AI, da fasahar manyan bayanai, da makamantansu.

Dawud ya ce, dandalin ya samar da muhimmiyar dama ga daliban, wadanda gabanin hakan suke fama da wahalhalu na rashin samun horo a matakai na kasa da kasa, da damammakin neman guraben ayyukan yi.

Huawei, wanda ke aiki tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilmin kasar Habasha, ya bude sassan nazarin fasahar zamani ta ICTs a manyan makarantun ilmi 42 a kasar Habasha. (Ahmad)