logo

HAUSA

Najeriya ta sha alwashin taimakawa yaki da ’yan fashin teku a mashigin tekun Guinea

2022-05-11 10:29:47 CMG Hausa

 

Babban daraktan hukumar lura da tsaron teku ta Najeriya ko NIMASA a takaice Bashir Jamoh ya ce, har kullum a shirye hukumarsa take, wajen samar da tsare-tsare, da manufofin da za su wanzar da nasarar yaki da ’yan fashin teku a mashigin tekun Guinea.

Bashir Jamoh, wanda ya sha alwashin hakan a jiya Talata, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na hadin gwiwar shiyya, don gane da batutuwan da suka shafi mashigin Guinea, wanda ya gudana a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, ya ce wanzar da nasarar dakile fashin teku, na da muhimmancin gaske tsakanin kasashen yammacin Afirka, kuma tare da hakan, za a rika la’akari da iyakoki da ikon kowace kasa, domin kaucewa duk wani sabani.

Jami’in ya ce hukumar NIMASA da rundunar sojojin ruwan Najeriya, a shirye suke su ci gaba da samar da dukkanin tallafi na hadin gwiwa da kasashen abokan hulda, ta yadda za a cimma nasarar wannan yaki da ’yan fashin teku.

Daga nan sai Jamoh ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen dake kewayen mashigin tekun Guinea, da hadin gwiwar sassan kasa da kasa. Yana mai bayyana hakan a matsayin abun da ya haifar da nasarar raguwar ayyukan ’yan fashin teku tun daga shekarar 2021. Ya kuma yi kira da a ci gaba da zage damtse, tare da aiwatar da ingantattun dabarun wanzar da wannan yaki.  (Saminu)