logo

HAUSA

Ya Kamata Harkar Tsaro Ta Kasance A Hannun Kasashen Turai

2022-05-11 21:32:59 CMG HAUSA

Ranar 9 da 10 ga wata, Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da shugaban gwamnatin kasar Jamus ta kafar bidiyo, tare da tattaunawa da takwaransa na kasar Faransa ta kafar tarho daya bayan daya, inda ya goyi bayan kasashen Turai da su tafiyar da harkar tsaro da kansu.

Watanni 2 da suka gabata ne shugabannin Faransa da Jamus suka bayyana a yayin taron koli da suka yi da Shugaba Xi Jinping ta kafar bidiyo cewa, yanzu kasashen Turai suna fuskantar rikici mafi muni, da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan babban yakin duniya na 2. Kasashen 2 suna goyon bayan warware batun Ukraine ta hanyar yin shawarwari, a kokarin samar da damar shimfida zaman lafiya. Amma tun bayan wannan lokaci, halin da ake ciki a tsakanin Rasha da Ukraine bai yi sauki ba, inda ma rikicin ya kara yin illa a wasu fannoni. Sakamakon rurar wutar da Amurka take yi, ya sa Turai ta rika sanya wa Rasha takunkumi, don haka Rasha ta mayar wa Turai martani mai karfi. Kasashen Turai suna fuskantar matsalar karancin abinci, karuwar ‘yan gudun hijira, da marasa aikin yi, da hauhawar farashin kaya, da matsalar tsaro da dai sauransu.

Hakika, dakile Turai da kuma hana Turai ta tafiyar da manyan tsare-tsarenta da kanta, su ne dalilan da suka sa Amurka ta rika rura wuta a tsakanin Rasha da Ukraine. Turai na kara bukatar basira da jarumtaka don samun tsaro, zaman lafiya da wadata. Kamar yadda kasar Sin ta fada, wajibi ne a yi taka tsan-tsan kan yin fito-na-fito tsakanin sassa daban daban, lamarin da zai kara kawo babbar barazana na dogon lokaci ga tsaro da kwanciyar hankali a duniya. Ra’ayin kasar Sin ya samu amincewar Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Yayin tattaunawar da ya yi da shugaba Xi Jinping ta wayar tarho, ya nuna cewa, Faransa da kungiyar EU na tsayawa tsayin daka kan tafiyar da manyan tsare-tsarensu da kansu, ba su amince kuma ba za su shiga rukunin yin fito-na-fito tsakanin sassa daban daban ba. (Tasallah Yuan)