logo

HAUSA

Tagwayen Hanyar Nairobi Da Sin Ta Gina Zai Fara Aiki Na Gwaji A Ranar 14 Ga Mayu

2022-05-11 21:30:13 CMG HAUSA

A matsayin muhimmin aikin hadin gwiwa na shawarar “ziri daya da hanya daya”, za a fara gwada amfani da tagwayen titin Nairobi, wanda kamfanin gina hanya da gajoji na kasar Sin ya zuba jari, raya, ginawa da sarrafa shi a ranar 14 ga watan Mayu.

Shi dai wannan titi, yana da tsawon kilomita 27.1 kuma ya hade da filin jirgin saman kasa da kasa na Jomo Kenyatta, da yankin kasuwanci na Nairobi, da fadar shugaban kasa da sauran sassa. Ana kuma fatan bayan bude titiin, zai taimaka wajen rage lokacin zirga-zirga a cikin birnin Nairobi.

Kwanakin da suka gabata ne, aka gudanar da gasar gudun Marathon ta birnin Nairobi na farko a wannan babbar hanya, inda sama da ‘yan wasa 8,000 suka halarta. Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya bayyana a wurin bikin mika lambar yabo cewa, za a kara inganta bangaren yawon bude ido, da harkokin kasuwanci, da zuba jari da sauran fannoni sakamakon bunkasar kayayyakin more rayuwa na zamani kamar tagwayen hanyar Nairobi . (Ibrahim)